Featured Post

Shin ko kasan menene lalacewar haqorii da kuma yadda zaka magance ta?


Lalacewar haƙori, wanda aka fi sani da kogonni (cavities), shine lokacin da haƙoranku suka lalace saboda ƙwayoyin acid da ƙwayoyin cuta suka yi. Idan ba'a kama shi da wuri an magance shi ba, zaku iya fuskantar matsala tare da wahala yayin cin abinci. Idan ba a kula da shi ba zai iya haifar da kumburin nama a kusa da haƙori, harma yakan janyo asarar hakori, da kamuwa da cuta ko ƙumburin kafa.


Yadda za a magance Lalacewar Hakori.  Fluoride na iya zama magani mai amfani akan sugars da acid da ke zuwa ta bakin mu a kullun. Yin amfani dashi, haƙoranku za su fi ƙarfi da lafiya fiye da kowane lokaci.


 Muna ba da shawarar cewa mutane su rika yin goga sau biyu a rana, daya da safe daya da rana, kuma su ziyarci likitan hakora a kalla duk bayan watanni 6 don tabbatar da cewa lalacewar hakora ba ta samu gindin zama a cikin bakinku ba.  Idan kun ji cewa kuna iya fuskantar faruwar ko alamun bayyanar ramin haƙori, to don Allah ka shirya kaje kaga likitan haƙori.


WAS THIS HELPFUL? 

Comments

Post a Comment